27 Janairu 2020 - 06:51
MDD Ta Yi Tir Da Karya Takunkumin Hana Shigar Makamai A Libiya

Tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD a kasar Libiya (UNSMIL), ta bayyana rashin jin dadi bisa yadda ake cigaba da karya dokar takunkumin hana yaduwar makamai a Libiya, yayin da ake cigaba da gwabza yaki tsakanin bangarorin dake yakar juna a Libiyar.

(ABNA24.com) A cewar sanarwa da tawagar ta (UNSMIL) ta fitar ta ce an ga wasu manyan jiragen saman dakon kaya da wasu jiragen sama sun sauka a filayen jiragen sama dake gabashi da yammacin Libiya, a cikin kwanakin nan inda suka sauke manyan makamai, da tankokin yaki, da masu bada shawara da kuma mayaka na bangarorin biyu, lamarin da a cewar MDD, zai iya jefa kasar cikin sabon tashin hankali da barkewar yaki.

Wannan dai na zuwa ne bayan da dukkan bangarorin da rikicin Libiyar ya shafa, suka amince zasu mutunta dokar takunkumin hana yaduwar makamai a Libiya wanda kwamitin sulhun MDD ya amince da ita, bayan wani taron kasa da kasa a ranar 19 ga watan Janairu nan, a birnin Berlin na kasar Jamus.

A ranar 12 ga watan nan ne bangarorin dake rikici a Libiya suka amince tsaigaita wuta a tsakaninsu a shiga tsakanin kasashen Rasha da Turkiyya.



/129